Translation English to Hausa story
The Generous Daughter
In a small village in Kano, Nigeria, there lived a kind-hearted Hausa girl named Aisha. She was the eldest child of Alhaji Abdullahi and Hajiya Fatima. Aisha was known throughout the village for her generosity and compassion.
One day, a severe drought hit the land, and many families in the village struggled to find food and water. Aisha's family was not exempt from the hardship. Despite their own struggles, Aisha convinced her parents to allow her to share what little food they had with their neighbors.
Aisha's selfless act did not go unnoticed. The villagers were touched by her kindness, and soon, people from all over the village were coming to Aisha's family for help. Alhaji Abdullahi and Hajiya Fatima were proud of their daughter's generosity and encouraged her to continue helping those in need.
As the drought persisted, Aisha's family faced even greater challenges. However, Aisha's kindness had inspired the entire village to come together and support one another. The villagers worked together to build a new well, which provided clean water for everyone.
The drought eventually ended, and the village was once again prosperous. Aisha's family was hailed as heroes, and Aisha's kindness was celebrated throughout the land.
Yarinya Mai Karamci
An yi wata yarinya bahaushiya mai kirki a wani karamin kauye a garin Kano Nigeria, ana ce mata Aisha. Ita ce babban diya ga Alhaji Abdullahi da Hajiya Fatima. Aisha ta shahara a duk fadin kauyen saboda karamci da tausayi.
Wata rana sai aka samu fari mai tsananin ya faɗo ƙasar, kuma iyalai da yawa a ƙauyen sun yi ta faman neman abinci da ruwa. Gidan su Aisha bai kubuta daga wahalan ba. Duk da wahalar da suke sha, sai da Aisha ta shawo kan iyayenta da su ba ta damar raba dan abincin da suke da shi da makwabta.
Ayyukan Aisha na rashin son kai ya dauke hankali mutane. Alherin nata ya ta6a mutanen garin, ba da jimawa ba jama'a daga ko'ina suna ta zuwa neman taimako a Gidan su Aisha. Alhaji Abdullahi da Hajiya Fatima sun yi alfahari da karamcin ‘yarsu kuma sun karfafa mata gwiwa da ta ci gaba da taimaka wa mabukata.
Yayin da fari ya ci gaba, dangin Aisha sun fuskanci kalubale mafi girma. Sai dai kuma alherin da Aisha ta nuna ya sanya al’ummar kauyen sun dau darasi su hadu su tallafawa juna. Mutanen kauyen sun hada kai wajen gina sabuwar rijiya, wadda yake baya da ruwan sha tsaftatacce ga kowa.
Daga karshe fari ya ƙare, kuma ƙauyen ya sake samun wadata. Iyalan A’isha sun kasance jarumai, kuma an yi alfahari da jin dadin ga ɗabiun Aisha a duk fadin kasar.